GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

‘Yan Bindiga Sun Sace Sabuwar Amarya, Mai Jego Da Wasu Mutane 11 A Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Sabuwar Amarya, Mai Jego Da Wasu Mutane 11 A Zamfara

40

- Advertisement -

‘Yan bindiga sun aukawa wani kauye a Zamfara inda suka yi awan gaba da mutane akalla 13, a ciki har da wata sabuwar amarya da masu jego.

 

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Zurmi da misalin karfe 11:45 na daren shekaran jiya Litinin.

 

Karanta: Matsafa Sun Yiwa Wasu Kananan Yara Yankar Gunduwa-gunduwa

 

Mazauna yankin sun bayyanawa manema labarai yadda ‘yan bindigar suka yi ta harbe-harbe domin su tsorata su.

Wani malamin makaranta mai suna Falalu Ashafa ya shaidawa manema labarai cewa matarshi, mahaifiyarshu da ‘yayanshi biyu na cikin wadanda aka sace.

 

Karanta: Za’a Takaita Tura Sakonni A WhatsApp Don Magance Labaran Bogi

 

Ya ce bayan harin, mutane 26 ne suka yi batan dabo, kuma ana kyautata zaton sace su aka yi.

Harin na zuwa kwanaki 2 kacal bayan da aka kai wani makamancinsa a karamar hukumar Birnin Magaji inda aka sace mutane 7.

 

Karanta: Wata Mata Ta Haihu A Wajen Gangamin Taron Yankin Neman Zaben PDP

 

Da aka tuntube rundunar ‘yan sandan jahar, mai magana da yawunta, Mohammed Shehu ya ce yan sanda sun samu nasarar dakile harin, amma daga bisani sun gano cewa ‘yan bindigar sun yi awan gaba da mutanen 13.

Leave A Reply

Your email address will not be published.