GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

‘Yan Bindiga Sun Wargaza Garuruwa Sama Da 98 A Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Wargaza Garuruwa Sama Da 98 A Jihar Zamfara

17

- Advertisement -

Mataimakin shugaban karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara, Alhaji Sani Galadima, ya bayyana cewa an yi watsa-watsa da Garuruwa da kauyuka fiye da 98 a sanadiyyar haren-haren ‘yan bindiga.

 

Karanta: ‘Yan Sanda Sun Harbe Dan Achaba Har Lahira A Kan Naira N200

 

Sani Galadima ya bayyana haka a lokacin da Ministan harkokin cikin-gida, Janar Abdurraham Dambazzau mai ritaya ya kai ziyara jihar domin ganewa idanuwansa irin barnar da ‘yan bindiga su ka yi a cikin ‘yan kwanakin nan.

Mataimakin shugaban karamar hukumar ya bayyanawa Ministan cewa zuba Sojoji da sauran jami’an tsaro da aka yi bai kawowa mutanen Yankin sauki ba. Jami’an tsaro ba su kawowa al’umma dauki a lokacin hari.

A jawabinsa, Sani Galadima, ya nemi a kawo karshen wannan bala’i kafin ya kai ga cin sauran manyan Birane da Garuruwan Zamfara.

 

Karanta: Maganin Harbin Kunama

 

Abdurrahaman Dambazzau kuma a na shi bangaren, yace gwamnati na yin bakin kokarin ta, ta’adin ‘yan bindigan yana cikin manyan abubuwan da ke ci wa gwamnati tuwo a kwarya, kuma tuni shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su kawo karshen matsalar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.