GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

‘Yan Sa Kai A Katsina Aun Nausa Daji Don Tunkarar ‘Yan Ta’addan Da Suka Addabi Yankin

‘Yan Sa Kai A Katsina Aun Nausa Daji Don Tunkarar ‘Yan Ta’addan Da Suka Addabi Yankin

103

- Advertisement -

Akalla mutune dari biyar ne ‘yan sa kai wadanda suka fito daga yankunan Sabuwa, Faskari, Kankara da Birnin Gwari suka yi gangami tare da shiga daji domin tunkarar ‘yan ta’adda masu garkuwa da kuma kashe mutane a wannan yankin.

 

Karanta: Kisan Zamfara: Zamfarawa Ba Sa Kwana A Gidajen Su Yanzu- Marafa

 

Sai dai labarin da muke samu ba dadin ji domin ‘yan ta’addar sun kashe kimanin mutane sama da sittin da daya (61) daga yankin Sabuwa da Kankara.

 

Wani ganau ya ce a yankin Sayau dake Dungun Mu’azu sun gano gawarwakin mutane akalla ashirin da daya, yayin da kimanin mutane goma sha biyar kuma sun bata ba as an inda suke ba.

 

‘Yan ta’addan dai suna cigaba da korar mutane daga garuruwansu. Kimanin Kauyuka goma sha daya ne duk sun gudu Smsun bar garuruwan nasu sakamakon ta’addancin wadannan mutanen.

 

Karanta: Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 23, sun cafke 18, tare da kubutar da mutane 40 a Zamfara

 

Jama’ar garin Dungun Mu’azu sun ce suna zargin jami’an tsaron Soja da kin daukar matakin da ya kamata wajen tunkarar wadannan miyagun, sun ce tsakanin wajen da Sojojin suke da inda ‘yan ta’addan suke bai wuce kilo mita biyu zuwa uku ba amma idan jama’a sun kai masu koke tare da sanar da su zuwan ‘yan ta’adan ba sa zuwa ko kuma su ce baa ba su umarni ba daga sama, hakan nan ne ya yi sanadiyyar al’umma ta tari aradu da ka domin tunkarar wadannan mutanen da kansu.

 

A wannan artabun dai ana kiyasta cewa Jama’ar Gari sunyi Saar Hallaka Hilanin kimanin su Arba’in, inda su kuma suka kashe Mutan gari yan sakai kimanin sittin da Daya a wannan Arangamar.

 

Kakakin Rundunar Yansandan Najeriya Yankin Jahar Katsina ya tabbatar da arangamar sai dai ya musanta yawan wadanda suka Rasa Rayukan nasu a Artabun, ya kuma tabbatar da cewa an Tura Runduna ta Musamman a wannan yankin domin kulawa da yankin.

 

Karanta: Tuna Baya: Abunda Ya Sa Na Sauka Daga Kujerar Mulki A Shekara Ta 2015 – Jonathan

 

Mazauna wannan yankin sun tabbatar da zuwan jami’an tsaron tare da cewa suna nan a garin Dandume suna ta harbe-harbe cikin gari har yanzu ba su kai ga shiga cikin Dajin ba inda ‘yan ta’addan suke.

Leave A Reply

Your email address will not be published.