GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Yusuf Tare Da Abokinsa Sun Yi Tattaki Daga Minna Zuwa Abuja Don Taya Hon. Abdullahi Murnar Lashe Zabe (hotuna)

Yusuf Tare Da Abokinsa Sun Yi Tattaki Daga Minna Zuwa Abuja Don Taya Hon. Abdullahi Murnar Lashe Zabe (hotuna)

135

- Advertisement -

Yusuf Burodo tare da abokinsa sun dauke alkawarin yin tattaki daga birnin Minna zuwa birnin tarayya Abuja domin ganin dan majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Kontagora/Wushishi/Mariga/Mashegu, Hon. Abdullahi Idris Garba (AIG) wanda aka fi sani da suna MAI SOLAR  idan har ya samu nasaran lashe zaben da majalisar wakilai na karo 4.

 

Karanta:  Zaben Gwamnan Jahar Neja: Dan Majalisa Abdullahi Ya Taya Gwamna Bello Murnar Lashe Zabe

 

Yusuf tare da abokinsa wanda suka kasance magoya bayan dan majalisan sun samu tabar dan majalisar da kansa. Dan majalisa Hon. Abdullahi Idris Garba (AIG) ya ji dadin ganinsu

 

A yayin da ya ke magana Yusuf tare da abokinsa, Hon.  Abdullahi ya ce “Abun ya ba ni matukar mamaki da na samu labarin cewa Yusuf da abokinsa suna tattaki domin taya murnar sake lashe zabe, ban taba tsammanin ina matukar masoya irin haka ba. Babu kalman da zan iya amfani da shi wajen nuna farin ciki na  game da hakan, a gaskiya na ji dadin tarbar wadannan masoyan nawa, ina matukar farin ciki. Na gode kwarai dagaske.”

 

Read: Zaben Gwamnoni: Hon. Abdullahi Ya Sake Kira Ga Al’ummar Mazabarsa Da Su Kauracewa Rikicin Zabe

 

Yusuf a yayin da yake magana da manema labarai a mamadin kansa da abokinsa bayan ya gama ganawa da dan majalisan ya ce:

 

“Mu kan yi tattaki daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma. Mu kan fara tafiyar daga inda mu ka tsinci kan mu kuma da zaran yamma karfe 6:00 daidai sai mu tsaya mu huta kafin mu ci gaba washe gari. Mun yi tattakin kwanaki 2 zuwa birnin tarayya Abuja.

 

Karanta: Kotu Ta Tabbatar Da Hon. Abdullahi A Matsayin Dan Takarar Majalisar Wakilai Na APC

 

Ni da aboki na mun dauka alkawari tsakanin mu da Allah da yayi mu a kan cewa za mu yi wannan tattakin idan har dan majalisan ya samu nasaran lashe zabe na karo na hudu (4). Babu shakka Hon. Abdullahi Idris Garba (AIG) shugaba ne nagari wanda ya san ya kamata saboda haka ina kira da sauran ‘yan majalisa da su yi koyi da shi.

 

A karshe kuma ina rokon Allah ya taya shi riko. #amin

 

Ga hotunan a kasa;

Leave A Reply

Your email address will not be published.