GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Za a Fara Daure Mabarata Da Masu Bada Sadaka

Za a Fara Daure Mabarata Da Masu Bada Sadaka

36

- Advertisement -

Kansiloli na birnin Kampala da ke kasar Uganda sun kafa sabuwar dokar haramta yin bara a fadin garin, musamman a gurin yara da tsoffi da ke gagaramba suna bara a titinan garin.

 

Karanta: An Sace Mutane Sama Da 30 A Kwanaki Biyu Kacal A Hanyar Kaduna-Abuja

 

Yin talla da bara a gurin yara ‘yan kasa da shekara bakwai akan titinan garin abu ne da aka saba gani.

Gwamnati ta ce akwai yara fiye da 15,000 ‘yan tsakanin shekara bakwai zuwa 17 da ke yawo kan titi suna bara, kuma a kullum adadin karuwa yake.

Banda hana bara da bada sadaka, dokar ta kuma haramta fataucin yara daga kauyuka zuwa birni da kama gida dominsu.

Haka zalika ta haramta wa manya sayar da kayayyaki kan titi a birnin.

 

Karanta: Facebook Na Shirin Fito Fa Hanyar Da Mutane Za Su Gane Masu Sonsu A Boye

 

Duk wanda aka kama ya na yin bara ko bada sadakar abinci ko kudi ga yaro akan titinan Kampala, zai shafe watanni shida a gidan yari, sannan za a ci tarar shi kudi dala $11 wato kimanin naira 4,000 kenan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.