GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Zaben Kano: Ina Da Tabbacin Samun Nasarar Lashe Zaɓen Da Za’a Sake – In Ji Gwamna Ganduje

Zaben Kano: Ina Da Tabbacin Samun Nasarar Lashe Zaɓen Da Za'a Sake - In Ji Gwamna Ganduje

28

- Advertisement -

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana farin cikinsa bisa yadda aka gudanar da zaben Gwamnan da ya gabata.

 

Karanta: Gargadi: Masu Fama Da Ciwon Ido Su Guji Amfani Da Ruwan Albasa – Masana

 

Gwamna Ganduje ya tabbatarwa da al’ummar Kano cewa ya na da ƙarfin guiwar lashe zaɓen da za’a sake gudanarwa ranar 23 ga watan March, 2019 wanda ake sa ran gudanarwa a wuraren da Hukumar Zabe mai zaman Kanta (INEC) ta bayyana.

 

Gwamnan ya jinjinawa masu kaɗa ƙuri’a bisa yadda suka yi fitar ɗango a ranar zaɓen, musamman yadda suka aminta da kadawa Jam’iyyar APC ƙuri’a, lallai mun tabbatar da cikakken goyon bayan al’ummar Kano ganin yadda dogwayen layuka suka cika akwatunan kada kuri’a, a cewar Gwamna Ganduje.

 

 

Karanta: Siyasar Kano: Dalilina Na Son A Sake Zaben Gwamna Ganduje – Inji Sheik Kabiru Gombe

 

Tun da farko dai Gwamnan na wannan jawabi ne jim kadan da dawowarsa daga babban birnin tarayya Abuja inda ya kai ziyarar kwana guda wanda daman haka yake cikin tsare tsarensa na ziyartar Abuja.

 

Ya ce kamar yadda kowa ya sani Hukumar zaɓe mai zaman Kanta (INEC) ta sanya ranar 23 ga watan Maris ya kasance ranar da za a sake zaɓe a wasu akwatunan zaɓe a Jihar Kano. Saboda haka Gwamna Ganduje ya tabbatarwa Jama’a cewa da yardar Allah madaukakin Sarki Jam’iyyar APC zata samu gagarumar nasara a zaben da za a sake gudanarwa.

 

 

Karanta: Babban Hadimin Ganduje Ya Ajiye Aikinsa Sabo Da Gwamnan Ya Ƙi Karɓar Ƙaddara

 

A karshe Ganduje ya ƙara miƙa Godiya ga kowa da kowa tare da fatan za a gudanar da wannan zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Leave A Reply

Your email address will not be published.