GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Zaben Kano: Kanawa Sun Kullaci Shugaban Buhari Suna Ta Shan Alwashi

Zaben Kano: Kanawa Sun Kullaci Shugaban Buhari Suna Ta Shan Alwashi

343

- Advertisement -

Al’ummar Jihar Kano musamman tsagin Darikar Kwankwasiyya da kuma masu yima Abba K Yusuf Soyayya ta musamman sun kullaci shugaban kasa Muhammad Buhari game da yadda aka gudanar da zaben Gwamnan Jihar Kano.

 

Karanta: Akwai Yiwuwar Za’a Sake Sabon Zaben Shugaban Kasa A Najeriya

 

Abun mamaki su Ya’yan Jam’iyyar PDP kachokan laifi suka dauka suka dorawa shugaban kasa Muhammad Buhari, cewar su yana sane aka murde zaben Kano aka baiwa Ganduje, idan ma bai sani ba amma ai yaga abubuwan da suka faru a jihar Kanon ranar zabe a sabbin kafafen sadarwa, idan ma ba haka bai ai yana da labarin sauye-sauyen Jami’an tsaron da aka yi a jihar don a shirya Titimurmura, duk mai yasa ya kame bakin sa, babu wata hujja da zata iya wanke Buhari a wajen mu ya yaudare mu.

 

 

Karanta: Wata Mata Ta Haifi Tagwaye Masu Ubanni Daban-daban

 

Wata matashiyar budurwa wacce ta kai munzalin Aure ita ta bayyana haka a wani Faifayin Bidiyo data fitar, tace Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi musu bazata sun narka mishi Kuri’u shi kuma yaci Amanar su.

 

A cikin maganganun nata har tana shan Alwashin cewar ina ma Buhari zai sake tsayawa takara hmmmm daya sha Mamaki.

 

 

Karanta: Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Cp Muhammad Wakili Ya Dawo Bakin Aiki

 

Ba ita kadai ce ba take da wannan korafin akwai Al’umma da dama a Kanon Wanda har yanzu suke kan bakar su da cewar ba Ganduje yaci zabe ba Abba ne yaci zabe murdiya kawai aka yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.