GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Zaben Kano: Tawagar Lauyoyin Jam’iyyar APC Sun Shirya Tsaf Domin Kare Nasarar Gwamna Ganduje

Zaben Kano: Tawagar Lauyoyin Jam'iyyar APC Sun Shirya Tsaf Domin Kare Nasarar Gwamna Ganduje

25

- Advertisement -

Tawagar lauyoyin jam’iyyar APC a jihar Kano sun bayyana shirinsu na kare nasarar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaɓen da ya gabata.

 

Karanta: Dandazon Ƙudan Zuma Ya Kashe Wani Jami’in Hukumar Kwastan

 

Tun da farko dai hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa wato INEC ce ta bayyana Gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka sake a jihar Kano a ranar 23 ga watan Maris.

 

Kakakin Lauyoyin Ma’aruf Mohammed Yakasai, ya sanar da matsayar Jam’iyyar APC a lokacin da yake jawabi a taron manema labarai da ya gudana a jihar Kano.

 

Ya ƙara da cewa tawagar lauyoyin sun gano cewa akwai buƙatar yin bayanin matsaya domin mutunta roƙon da jam’iyyar PDP ta yi a gaban kotun, wanda kuma kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta bayar da damar duba kayayyakin zabe da aka yi amfani da su a jihar Kano.

 

 

Karanta: EFCC: Kotu Ta Baiwa Shekarau Iznin Tafiya Umara

 

Ma’aruf Yakasai ya ce tawagar lauyoyin jam’iyyar APC sun shirya domin kare nasarar da Gwamna Ganduje ya samu a gaban kotun zaɓen wacce ta fara zama a ranar Talata.

 

Ya ci gaba da cewa jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje sun shirya tsaf domin kare ƙuri’un da mutanen jihar suka baiwa jam’iyyar APC a Zaɓen da ya gabata.

 

Karanta: Shekaru 30 Na Mulkin Omar Hassan Al Bashir A Ƙasar Sudan

 

A ƙarshe Ma’aruf Yakasai ya bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar PDP Injiniya Abba Kabir-Yusuf ba shi da wani dalili da zai ƙalubalanci nasarar da Gwamna Ganduje ya yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.