GULMAWUYA
Bringing together nigerian community through culture

Zamu Gudanar Da Zaben Gaskiya Da Gaskiya A Jahar Kano – INEC

Zamu Gudanar Da Zaben Gaskiya Da Gaskiya A Jahar Kano – INEC

19

- Advertisement -

 

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta bada tabbacin shirya zaben gaskiya da adalci a zaben maimaici da zata gudanar a jahar Kano a ranar 23 ga watan Maris, kamar yadda shugaban hukumar reshen jahar Kano, Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya bayyana.

 

Karanta: Ko Da Tsiya Sai APC Ta Lashe Zaben Gwamnan Kano – Inji Shugaban APC Na Jihar Kano

 

Majiyar mu ta ruwaito Riskuwa na fadin hukumar ta dauki wannan mataki ne sakamakon rikice rikicen da aka samu a wasu akwatuna, da kuma matsalar aringizon kuri’u, wanda hakan yasa aka soke zaben a wasu rumfuna 210 cikin kananan hukumomi 22.

 

Karanta: Dalilin Sake Zaben Gwamnan Jahar Kano Zagaye Na Biyu

 

“Ina sanar da jama’a cewa a ranar Asabar, 23 ga watan Maris ne zamu gudanar da wannan zabe, kuma zamu tabbatar ya gudana cikin gaskiya da adalci. Zaben ya shafi rumfunan zabe 210, a mazabu 88 dake da kuri’u 128,572.” Inji shi.

 

Karanta: Wani Mutum Ya Sace Shanu 150 Ya Yanka Guda 50 a Ciki

 

A zaben makon daya gabata, dan takarar jam’iyyar PDP, Abba gida gida ya samu kuri’u 1,014,474, yayin da dan takarar jam’iyyar APC, Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu 987,819, bambancin kuri’u 26,655, wanda bai kai adadin lalatattun kuri’u 128,572 ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.